Shugabanni ba su da Rigar Kariya a Shari’ar Musulunci – Pantami

 

Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, farfesa Isa Ali Pantami ya yi kira da a yi watsi da tsarin ba shugabanni rigar kariya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Pantami ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Abuja a wajen taron shekara-shekara na cibiyar Musulmi wato the Muslim Congress (TMC) mai taken; ‘Gina ingantacciyar ƙasa: Nauyi ne kan shugabanni da mabiya domin tuna ranar ƴancin Najeriya na 64.

“A Musulunci, babu wata rigar kariya domin kariyar za ta ba mutum wata dama ce kawai a lokacin da yake shugabanci, wanda ba za ka samu ba, bayan ka bar ofis. Wasu lokutan kariyar na da kyau, amma a wasu lokutan hakan na jawo maka matsaloli da yawa ne,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa, “da zarar ka bar ofis bayan shekara huɗu ko takwas sai ka ga ana ƙalubalantakarka da tuhume-tuhume da dama, wasu har guda 120 ma. Don haka kariyar ba ta hana mutum fuskantar shari’a, kawai tana jawo kawo jinkiri ne da kuma ba mutum damar ƙara aikata wasu laifukan.

“A shari’ar Musulunci babu wata rigar kariya. Da shugaba da mabiya kowa zai iya fuskantar shari’a, kuma dole ya je ya kare kansa. An yi wa Ali ibn Abi Talib da Umar ibn Khatab suna Khalifanci. Don haka yana da kyau a samar da daidaito a wajen shari’a,” in ji Pantami.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here