Sojaboy: Matashin ya Rabu da Baturiyar Matarsa Sa’ar Mahaifiyarsa

Usman Umar ya caccaki tsohuwar matarsa, Lisa Hamme, bayan aurensu ya mutu.

Mawakin dan Najeriya ya daura bidiyon daurin aurensu inda yake godewa Allah da ya ceceshi.

Umar ya auri Lisa wacce ta girmesa da shekaru 23 duk da fadace-fadacen da sukeyi yayin soyayya.

Masoyan biyu sun soki juna yayinda suka rabu.

Mawaki dan Najeriya, Usman Umar, wanda akafi sani da Soja Boy, ya jefa abin magana cikin jama’a yayinda ya caccaki tsohuwar matarsa, Lisa Hamme.

A bidiyon da ya daura a shafinsa na Instagram, Soja Boy ya bayyana yadda ya rabu da ita kuma yana godewa Allah da ya ‘yantar da shi daga hannunta.

Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta nuna rashin jin dadinda da auren mace sa’arta wacce ta girmeshi da shekaru 23.

Usman ya godewa Allah kuma yace da alamun asiri tayi masa.

Yace: “Ko dai an yaudarni ko kuma an yi mi asiri, kalli fuskar mahaifiyata da dan’uwana, gaba daya basu ji dadi ba amma a haka na cigaba. Na godewa mai sama da ya ‘yantar da ni.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here