Dakarun Sojojin Najeriya Sun Kama Hatsabibin Dillalin Bindigu

Dakarun Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin bindigu da sunansa ke cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Manjo Janar Benard Onyeuko, Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya ne ya sanar da hakan yana mai cewa a Jihar Taraba aka kama shi.

Onyeuko ya kara da cewa sojojin sun kama wani dan bindiga mai shekara 65 mai suna Ichen Igbaka da matarsa Salomi Gbaka.

Jihar Taraba – Dakarun Sojoji na Operation Whirl Stroke, ta ce ta kama wani hatsabibin dilallin bindigu, Ardo Manu Abdulrahaman Maranello, wanda jami’an tsaro ke nema a jallo.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kama shi ne a Jihar Taraba.

Direkatan Sashi Watsa Labarai na Sojoji, Manjo Janar Benard Onyeuko, wanda ya bayyana hakan a jiya a Abuja, ya ce Marenewa ya kware wurin sayarwa da bada hayan bindiga ga yan bindiga da masu garkuwa.

Ya yi bayanin cewa dakarun sojojin sun kai samame mabuyar yan ta’adda da ke a Maraba a Ukyonugu Ityuluv a karamar hukumar Ukum a Jihar Benue.

Sojoji sun kama dan bindiga mai shekara 65

Onyeuko ya bayyana yadda sojojin suka kuma kama wani dan bindiga mai shekara 65 mai suna Ichen Igbaka da matarsa Salomi Gbaka.

Ya kuma ce sojojin na FOB Bakura na Operation Hadarin Daji sun amsa kirar neman dauki daga Rain Dankura a karamar hukumar Bakura a Jihar Zamfara suka yi musayar wuta da yan bindiga bayan sun sace wasu fararen hula.

“Bayan artabun, yan bindigan sun ceto fararen hula guda shida suka kuma kashe yan ta’adda biyu.

“Abubuwan da aka kwato sun hada da AK-47, gurneti na hannu guda 36, wayoyin salula biyu da N211,915,” ya kara.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here