Sojoji Sun Kama Masu Kaiwa Boko Haram Sinadaren Hada Bom a Borno da Yobe

 

Dakarun Sojojin Najeriya sun samu nasarar damke masu kaiwa Boko Haram sinadaren hada Bom.

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun damke dan Boko Haram da aka dade ana nema.

An kama buhuhunan sinadarin Urea kimamin 300 da ake amfani wajen hada Bam.

Abuja – Hukumar Sojojin Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin dan Boko Haram a Arewa maso gabas kuma ta kai simame ma’ajiyar sinadaran hada bama-bamai a Borno da Yobe.

Diraktan hulda da jama’a na hukumar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabin da ya saki a shafin Facebook.

Yace wannan nasara ya biyo bayan hare-haren da rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) suka kai.

Yace:

“Dakarun Sector 2 Joint Task Force na Operation HADIN KAI (OPHK) sun damke wani babban dan Boko Haram kuma sun kai simame ma’ajiyar ajiyan sinadaran hada boma-bomai a Damboa dake jahar Borno; da kuma Gashua dake jahar Yobe.”

“Sakamakon cinne, an damke wani dan ta’addan BH/ISWAP da aka dade ana nema ruwa a jallo a hanyar Damboa-Wajiroko.”

Ya kara da cewa Sojoji sun kwato buhuhunan sinadarin Urea 281 a ma’ajiyoyi daban-daban kuma an damke masu kaiwa Boko Haram wadannan kayayyaki mutum biyu.

Yace:

“Hakazalika, Sojoji sun samu nasarar damke wasu masu kaiwa yan ta’adda sinadaran hada boma-bomai. Kasuwar ta shahara da taya yan Boko Haram boye sinadaren.” “A harin da aka kai, an damke buhuhunan Urea 281 daga kasuwar kuma an damke masu sayarwa Boko Haram.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here