Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram a Jahar Borno
Zakakuran sojojin Najeriya na cigaba da samun nasarori a yaki da ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas.
Horarrun sojojin cikin kwanakin nan suka sheke wasu mayakan Boko haram a jahar Borno.
An halaka ‘yan ta’addan ne bayan an kama su suna dasa bama-bamai a kan hanyar wucewar sojojin Najeriya Zakakuran sojojin sashi na 1 karkashin rundunar Operation Lafiya Dole sun halaka wasu mayakan ta’addanci na Boko Haram a hanyar Njimia dake Alafa, kusa da dajin Sambisa dake jahar Borno.
Kwamandan runduna ta musamman ta 21 dake Bama, Waidi Shayibu, ya jagoranci aikin.
Read Also:
An halaka ‘yan ta’addan yayin da suka dasa abubuwa masu fashewa a hanyar da dakarun sojin ke bi. Jami’in sirrin da ya bukaci a boye sunansa ya sanar da PR Nigeria cewa ‘yan ta’adda kadan ne suka tsere da miyagun raunika.
A kalamansa:
“Kamar yadda muka saba hadin guiwa tsakanin dakarun sojin sama da na kasa, rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukan mayakan Boko Haram a wasu hanyoyi.
“A lokacin da muka samu tabbaci, dakarunmu sun yi lambo yayin da suka hango su sannan suka bi su da ruwan wuta.
An samu gawawwakin ‘yan ta’adda 7, bindigoginsu, bindigar harbo jirgin sama da babura.
“An samu wasu abubuwa masu fashewa a gefen tituna kuma sojojin sun lalata su.”