Sojojin Najeriya Sunyi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Boko Haram

Rundunar Operation Fire Ball suna cigaba da samun nasarar ragargazar ‘yan ta’adda a Maiduguri.

Rundunar ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 23, wurin ceto wasu mutane 5 daga hannun ‘yan Boko Haram.

Kamar yadda mukaddashin jami’in hulda da jama’a, Birgediya janar Benerd Onyeuko ya tabbatar.

Rundunar Operation Fire Ball ta arewa maso gabas ta ragargaji ‘yan bindiga 23, sannan ta kwashe wani abu mai fashewa a hannunsu, wuraren Ngamdu, kusa da Maiduguri.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda yace wasu daga cikin ‘yan bindigan sun sha ragargaza yayin kokarin amsar kudaden fansa daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu.

A cewarsa, sojojin sun samu nasarar ceton wasu mata 2 da yara 3 a hannun ‘yan Boko Haram, Vanguard ta wallafa.

A cewarsa, an samu bindigogi AK-47 guda 8, bindiga mai jigida, bindigogin yaki da sauran miyagun makamai bayan kashesu.

Rundunar Operation Fire Ball suna cigaba da samun nasarar yin ayyuka tukuru a yankin. A cikin kankanin lokaci sun samu nasara mara misaltuwa.

Sakamakon ragargazar, sojoji 6 sun ji munanan raunuka, amma suna asibitin sojoji suna samun sauki.

Onyeuko ya roki mazauna yankin da su bai wa sojojin hadin kai, don samun damar sanin shige da ficen ‘yan ta’addan da maboyarsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here