Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5 a Jahar Benue

 

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari garin Anune a karamar hukumar Makurdi ta jahar Benuwe.

Sai dai kuma, sojojin Najeriya sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’addan inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Wasu jami’an ‘yan sandan Najeriya sun bukaci al’ummar Benuwe da su guji karya doka da oda Sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wasu yan fashi da makami.

su biyar da suka kai hari kan wani gari a ƙaramar hukumar Makurdi ta jahar Benuwe, Daily Trust ta ruwaito. Jaridar ta ce sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan fashin a kan iyakokin jahohin Benuwe da Nasarawa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun farma mazauna kauyen Anune, wani garin karkara a wajen karamar hukumar Makurdi, kuma sun kashe wasu mutane da ba a bayyana adadin su ba.

Wani ganau ya ce an ga wani jirgin sojin sama mai saukar ungulu yana shawagi a kusa da kauyen da abin ya shafa tsakanin karfe 9 na safe zuwa 10 na safiyar Asabar, a daidai lokacin da sojoji da ‘yan sanda ke ta yawo a cikin manyan motoci.

Shaidar ya kara da cewa jami’an tsaro sun shiga cikin dajin da ‘yan ta’addan suka tsere sannan kuma ba da dadewa ba, sai aka ga sojoji ’sun dawo tare da akalla gawarwakin mutane biyar da ake zargin na yan fashin ne.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sanda a jahar Benuwe, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da harin kan kauyen Anune amma ba ta bayyana ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ba.

Anene ta ce an tura tawagar jami’an ‘yan sanda yankin don dakile ci gaba da karya doka da oda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here