Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Kama 114 Cikin Mako Daya
Gwarazan dakarun sojin Najeriya sun halaka gwamman ‘yan ta’adda a shiyyoyin arewa uku cikin mako ɗaya.
Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa akalla ‘yan ta’adda 50 ne suka sheƙa barzahu yayin da sojojin suka ceto mutane 49.
Ta ce a tsawon mako ɗaya, sojojin sun kama yan ta’adda sama da 100, yayin da wasu suka miƙa wuya a Yobe da Borno.
FCT Abuja – Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sanar da cewa dakarun sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 50 tare da kama wasu 114 cikin mako guda.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, DHQ ta ce sojin sun samu nasara ne a ayyuka daban-daban da suka gudanar a Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso yamma.
Daraktan yaɗa labarai na Hedkwatar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 49 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda, kamar yadda Channels tv ta tattaro.
Arewa maso Gabas
Read Also:
Ya ce rundunar Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas ta ci gaba da matsa wa ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, wanda ya tilasta wa wasu mayaƙa miƙa wuya a Yobe da Borno.
A cewarsa dakarun sojin sun kuma kwato makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar AK47 18, alburusai 137 da wayoyin hannu guda biyu.
“Sojojin sun kuma kashe ‘yan ta’adda 12, sun kama 26 tare da kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas,” in ji shi.
Arewa ta Tsakiya
Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven da ke Arewa ta tsakiya sun cafke masu garkuwa da mutane ne a kananan hukumomin Kanam da Sanga na jihohin Filato da Kaduna.
Ya ce dakarun sojin sun sheƙe yan ta’adda 2, suka kamo wasu 12, kana suka ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su. Sannan sun kwato makamai da kayan aiki.
“Jimulla, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda hudu, sun kama wasu 28 tare da kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Arewa ta Tsakiya.”
Arewa maso Yamma
A yankin Arewa maso Yamma, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kai same tare da sheƙe ‘yan ta’adda a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.
Kakakin DHQ ya ce a wani luguden wuta ta sama da aka yi a sansanin ɗan ta’adda, Kamilu Buzaru, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, an yi nasarar kashe wasu da dama daga cikin ‘yan ta’addan.