Adadin Sojojin Amurka da Suka Mutu a Harin Bam a Kasar Afghanistan
Gwamnatin Amurka ta bayyana adadin jami’an da ta rasa sakamakon harin Bam a Afghanistan.
Amurka na cigaba da kwasan yan kasarta da kuma wasu yan Afghanistan da suka taimaka mata.
Sunaye da hotuna wasu daga cikin Sojoji da aka kashe sun fito.
Amurka – Sunaye da hotunan jami’an Sojojin Amurka 13 da suka rasa rayukansu a harin kunar bakin wake da yan ta’addan ISKP suka kai wajen tashar jirgin Kabul ranar Alhamis sun fara fitowa.
An tura wadannan Sojoji ne don duba yadda ake kwasan yan Amurka daga Afghanistan.
Read Also:
Sunan wani jami’in Sojojin ruwa da Marine hudu sun fito yayinda har yanzu ba’a bayyana sunayen sauran Marine 6 da Sojojin kasa biyu ba saboda ba’a sanar da iyalansu ba tukun.
Mai magana da yawun rundunar Marine na Amurka, Manji Jim Stenger ya bayyanawa ThePost cewa:
“Muna cigaba da jimamin mutuwar wadannan jami’ai kuma muna addu’a ga iyalansu. Abinda muka mayar da hankali kai yanzu shine kula da iyalansu da kuma wadanda suka jikkata.”
Bisa tsarin Amurka, hukumar Sojoji ba ta sakin sunayen matattunsu sai bayan awanni 24 da sanar da iyalansu, amma wasu yan uwansu sun tabbatar da sunayen wasu daga cikinsu.
Ga jerin sunayen da suka bayyana kawo yanzu:
1. Maxton Soviak
2. Kareem Nikoui
3. David Lee Espinoza
4. Rylee McCollum
5. Jared Schmitz.