Adadin ‘Yan jarida da Sojojin Isra’ila Suka Kashe Cikin Shekara 21

 

Wata kungiya mai rajin kare lafiyar ‘yan jarida ta ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe ‘yan jarida akalla 20 tun daga shekara ta 2001, inda ta zargi sojojin kasar da kokarin kauce wa bincike.

Rahoton kungiyar ta Committee to Protect Journalists ya bayyana gazawa wajen gudanar da bincike yadda ya kamata a kan irin wadannan kashe-kashe.

Kuma a yanzu kungiyar na hankoron ganin an gudanar da bincike na zargin aikata miyagun laifuka a kan akalla uku daga cikin kisan na ‘yan jarida.

Sai dai sojin Isra’ilar sun ce suna martabawa tare da tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida kuma ba sa harin ‘yan jaridar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here