Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga a Dazukan Sokoto da Katsina
Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ɓarayin daji da dama tare da lalata maɓoyarsu a dazukan jahohin Sokoto da Katsina a yankin arewa maso yamma, kamar yadda jaridar intanet ta PRNigeria ta rawaito.
A jahar Sokoto sojojin ƙarƙashin shirin HADARIN DAJI sun kai hare-hare ne ta sama a dazukan Mashema da Yanfako da Gebe da Gatawa a ƙananan hukumomin Isaa da Sabon Birni.
Read Also:
Wata kafa ta sojojin Najeriyar ta sheda wa jaridar ta PR cewa an samu nasarar hakan ne a ruwan bama-bamai da suka yi ranar biyar ga watan Oktoba 2021, bayan binciken da aka yi ta yi ta sama inda aka gano wuraren da ɓarayin dajin ke zaune.
Rahotan ya bayyana cewa mutanen yankunan da aka kai hare-haren sun bayar da labarin cewa sun ga ɓarayin da ke tserewa sun fake a wata makarantar furamare a ƙauyen Bafarawa.
A jahar Katsina jaridar ta PRNigeria ta ce ta gano cewa jiragen yaƙin sama na Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maɓoyar ɓarayin a dajin Rugu da ke da iyaka da Karamar Hukumar Ƙanƙara a tsakanin ranar 30 ga watan Satumba da 3 ga watn Oktoba na wanan shekara.
A ɗaya daga cikin hare-haren an lalata sansanin wani ɗan ta’adda da ake kira Gajere inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma suka samu raunuka in ji rahoton jaridar.