ISWAP: Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan a Ngamdu
Wasu jiragen yakin sojin saman Najeriya sun dakile wani harin da kungiyar ISWAP ta shirya kai wa a garin Ngamdu mai iyaka da jahohin Yobe da Adamawa.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa baya ga Ngamdu maharan sun so kai hari a wani sansanin soji da ke yankin, kafin jiragen su yi musu luguden wuta.
Wata majiyar tsaro ta ce dama rundunar sojin Najeriya ta samu bayanan sirri cewa ISWAP na shirin kitsa hare-hare, kuma kungiyar ta tsara amfani da hanyar Goniri da Damboa don shiga Ngamdu.
Majiyar ta kara da cewa ” suna cikin tunkarowa ne sojoji suka bude musu wuta ta sama da kasa ta kashe su.”
Sai dai kawo yanzu babu sanarwar adadin mayakan ISWAP din da aka kashe a kwanton baunar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here