Rundunar Mayakan Sojojin Saman Najeriya ta Hallaka ‘Yan Bindiga 26 a Zamfara

 

Sojoji na cigaba da ruwan wuta kan bindiga a dazukan arewa.

Wannan ya biyo bayan datse layukan sadarwa a jahar Zamfara.

Yan bindiga sun fara arcewa daga Zamfara zuwa Sokoto.

Zamfara – Rundunar mayakan saman Najeriya NAF ta yi ruwan wuta kan tsagerun yan bindiga a dajin Baranda dake jahar Zamfara kuma an hallaka manyan tsageru biyar.

PRNigeria ta rawaito cewa Sojoji sun hallaka yan bindigan ne yayinda suka kai sintiri wasu dazuka dake yankin Arewa maso yamma.

Manyan yan bindigan da aka kashe sun hada da Hussaini Rabe, Murtala Sabe, Basiru Nasiru, Sama da Isah.

An tattaro cewa wadannan yan bindiga yaran wasu kwamanda tsageru ne mai suna Abu Redde.

Wani mazauni garin wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa ruwan wutan da Sojoji suka yi a dazukan Tsaunin Sani dake Yantumaki a karamar hukumar Danmuwa yayi sanadiyar mutuwar yan bindiga akalla 26.

Ya kara da cewa an lalata babura 13 a harin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here