Rashin Sani: Rundunar Sojojin Sama ta Jefa Bam a Kan Masu Murnar ɗaurin Aure a Jahar Neja
irgin yaƙin rundunar sojojin sama yayi kuskuren jefa bam a kan wasu mutane dake taron murnar ɗaura aure.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da hakan, yace mazauna yankin biyu sun rasa rayuwarsu.
Rundunar sojojin sama (NAF) tace ba ta samu wani rahoto kan wannan kuskuren ba, manufarta yan bindiga ne da suka taru a yankin.
A wani harin bam da jirgin rundunar sojojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jahar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ɗaurin aure, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoton vanguard ya nuna cewa, an kashe yan bindiga da dama yayin wannan aiki na jirgin NAF.
Read Also:
Rahotanni sun bayyana cewa harin da jirgin yaƙin ya kai ya kashe wasu makiyaya dake aikin satar shanu, kuma jirgin ya taso ne daga sansanin sojoji dake jahar Katsina.
Sai dai an gano cewa ɗaya daga cikin bam ɗin da jirgin ya jefa ya dira a wurin taron murnar ɗaurin aure a Wani Ƙauyen jahar Neja, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar.
Shaidan yace: “Mun hangi wani jirgi na sakin bam a maɓoyar yan bindiga, amma ɗaya daga cikin bam ɗin ya sauka a wurin taron murnar ɗaura aure a ƙauyen Argida.”
“Biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun mutu, kuma mun gano cewa wasu baƙi da aka gayyato wajen taron sun ji raunuka.”
Amma da aka tuntuɓi kakakin rundunar sojojin sama, Edward Gabkwet, yace harin bam ɗin da suka gudanar ya tafi yadda ake so cikin nasara.
Yace:
“Ba a kawo mana wani rahoton cewa harin ya shafi waɗanda ba ruwan su ba, manufar mu ita ce yan bindigan dake yankin Genu.
Bayan mun samu rahoton fasaha cewa sun taru a yankin suna ƙulla shirin kaiwa mutane hari.”