Bayan Nada Sababbin Hafsoshin Tsaro: Sojojin Najeriya Sun Wargaza Sansanin ‘Yan Boko Haram

 

Sojojin Najeriya sun afkawa sansanin ‘yan ta’addan Boko Haram a dajin Sambisa.

Harin ya biyo bayan sa’o’i kadan da aka nada sabbin hafsoshin sojojin Najeriya.

Sojojin sun bayyana cewa sun wargaza sansanin ‘yan ta’adda 4 a yankin na Sambisa.

Sojojin Najeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce, MNJTF, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.

An bayyana nasarar ne ‘yan sa’o’i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja.

Aikin da Brig. Gen Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.

Wata majiyar soji ta fadawa PRNigeria cewa sansanonin sun kasance sansanin horar da mayakan kungiyar tare da girke dakaru masu shirin ko-ta-kwana a shirye-shiryen kai harin kwanton bauna a wuraren sojojin da ke kusa.

Majiyar ta ce an kashe wasu kwamandojin kungiyar ‘yan ta’addan da kuma mayaka masu yawan gaske, yayin da yawa kuma suka samu munanan raunuka yayin kai harin.

An kame dimbin kayan aiki daga hannun ‘yan ta’addan yayin da kayan abinci, Na’urar abubuwan fashewa, Bama-bamai, abubuwan dinkin kayan sawa duk an lalata su.

“Mun share Maiyanki, Darulsallam, Bula kurege kuma yanzu mun karbe Izza, dukkansu tsoffin wuraren Boko Haram ne masu karfi.

Sojojinmu sun sha kai hari mafakarsu, cikin dare, amma duk an fatattake su yayin da aka yiwa makiyan mummunar rauni.

Ya kuma bayyana cewa soja daya ne ya rasa rayuwarsa yayin da sojoji uku suka ji rauni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here