Kungiyar SOKAPU ta Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Yadda Rikon Lamarin ‘Yan Fashi da Makiyaya Dake Addabar Yankin Arewacin Najeriya

Wata fitacciyar kungiyar Kudancin Kaduna, SOKAPU, ta nemi gwamnatin tarayya da ta bayyana ‘yan fashi da makiyaya makasa a matsayin ‘yan ta’adda.

Shugaban kungiyar SOKAPU, Jonathan Asake, ya ce dole ne gwamnati ta sa kafar wando daya da ‘yan fashi kamar yadda ta ke yi da masu tayar da kayar baya a kudu.

Asake ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun ma fi hadari ga hadin kan Najeriya fiye da masu son ballewa da gwamnatin ta ke amfani da dukkan karfinta wajen yakarsu.

Kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take rikon lamarin ‘yan fashi da makiyaya da ke addabar yankin arewacin kasar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta arewa ta bukaci gwamnati da ta yi amfani da irin dabarun da aka bi wajen kamo shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, da kuma dan rajin kare kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho, wajen magance matsalar. ‘yan fashi.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kungiyar SOKAPU na kasa, Jonathan Asake, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli.

‘Yan fashi sun fi zama barazana ga hadin kan Najeriya fiye da masu son ballewa Asake ya bukaci gwamnati da ta daina lallaba ‘yan fashi da makami a arewacin kasar, yana mai lura da cewa ayyukansu na barazana ga hadin kan Najeriya fiye da masu neman ballewa.

Da yake ci gaba da magana, Asake ya ce kungiyar ta gamsu ba tare da wata shakka ba cewa gwamnati na da karfin da za ta iya yaki da barayi wadanda suka sanya rayuwar ‘yan kasa cikin wani yanayi.

Ya ce yadda gwamnatin tarayya ta ke maganin ‘yan bindigar Benuwai, Terwase Akwaza, aka Gana, Kanu, Igboho da sauransu ya nuna cewa tana da isasshen karfin da za ta yi maganin ‘yan fas.

Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin nuna matakan da suka dace na tunkarar ‘yan fashin ko da bayan wasun su sun harbi wani jirgin sama a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.

A ayyana ‘yan bindiga, makasan makiyaya a matsayin yan ta’adda SOKAPU ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta hanzarta bayyana ‘yan fashi da makami da masu satar mutane a matsayin ‘yan ta’adda.

A cewar Asake, ayyukan ‘yan ta’addan sun jefa mutane cikin wani mawuyacin hali tare da lalata gonaki, jaridar Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ayyana wadannan Fulani makiyaya masu dauke da makamai, masu satar mutane da ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here