Gobara: Gwamnatin Sokoto ta Gargaɗi Mata kan Amfani da Gas
Gwamnatin jihar Sokoto, ta yi kira ga matan jihar su zama masu kula da mai da hankali yayin girki da tukwanen gas.
Read Also:
Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayyana haka lokacin ziyarar jaje bayan wata gobara ta tashi a yankin Igwai har ta yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin hadimansa.
Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne sanadin girki da gas, lamarin da ya kai ga rasa ran da kuma asarar dukiya.
Ahmad Aliyu ya ce yana da kyau mata su ƙara kula sosai a lokacin da suke amfani da gas domin girki a cikin gidajensu.
A lokuta da dama dai gas ɗin girki kan haddasa gobara a wasu sassan Najeriya, lamarin da a wasu lokutan kan zo da asarar rayuka.






