Mataimakin Gwamnan Sokoto ta Musanta Raɗe-Raɗin Fita Daga Jam’iyyar PDP

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Mannir Dan’iya ya musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party mai mulkin jihar.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru a ofishin mataimakin gwamnan, Aminu Abdullahi Abubakar, ta bayyana raɗe-raɗin a matsayin maras tushe.

Ta ƙara da cewa “har yanzu Hon Mannir Dan’iya ɗan jam’iyyar PDP ne, kuma yana ci gaba da jaddada goyon bayansa gare ta.”

Raɗe-raɗin ficewar mataimakin gwamnan daga jam’iyyar PDP na zuwa ne bayan sauya sheƙar ɗaya daga cikin makusantansa, Ummarun Kwabo, daga jam’iyyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here