Ma’aikatan Ceto a Spain na Neman ‘Yan Cirani 21 da Suka Nutse a Ruwa
Ma’aikatan ceto a kudu maso yammacin ƙasar Spain na neman ‘yan cirani 21 da suka ɓata bayan jirgin ruwansu ya kife a tekun Cape Trafalgar.
Ya zuwa yanzu an gano gawar mutum hudu.
Wasu mutun uku da suka tsira sun ce mutum 28 da suka fito daga arewacin Afrika ne ke cikin jirgin ruwan roba da ya tashi daga Morocco.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya gano jirgin ruwan da kan nutse a ruwa bayan minti 40 wanda wani babban jirgin ruwa ya sanar da shi.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here