Ma’aikatan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a Shirin SPW Sun Koka Kan Rashin Biyan su Hakƙokinsu
Har yanzun gwamnatin tarayya bata biya mafi yawancin ma’aikatan SPW hakƙokin su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an biya wasu kuɗin wata ɗaya yayin da wasu ko sisi ba’a biya su ba.
A shekarar da ta gabata ne, shugaba Buhari ya amince da ɗaukar yan Najeriya marasa aikin yi 774,000 a faɗin Najeriya.
Dubbannin ma’aikatan da gwamnatin tarayya ta ɗauka a shirin SPW sun koka kan rashin biyan su Naira N20,000 na tsawon watanni uku, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa har yanzun mafi yawancin waɗanda aka ɗauka a tsarin aikin SPW na tsawon wata uku (Fabrairu-Afrilu) ba’a biya su N20,000 kamar yadda aka musu alƙawari ba.
A jahar Borno, wasu ma’aikatan sun ce sau ɗaya kacal aka biya su hakkinsu na Naira N20,000 Hajja Fanna, daga garin Gamboru, ƙaramar hukumar Ngala, tace har yanzun tana jiran ragowar kuɗinta N40,000 na watanni 2.
Wani mutumi daga ƙaramar hukumar Jere, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace yayi aiki a tsarin amma har yanzun ba’a biya shi ko sisi ba.
Shugabar NDE ta jahar Borno tace ya kamata ace kowa ya samu N20,000 duk wata.
Read Also:
Shugaban NDE reshen jahar Borno, Mrs Mairo Aliyu, tace an ɗauki marasa aikin yi 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma 27 da ake da su a Borno.
Ta kuma tabbatar da cewa ya kamata ace dukan ma’aikatan an biya su N20,000 har na tsawon wata uku, duk kuwa da cewa watannin da aka ware domin aikin sun wuce.
Ta bayyana cewa matsalolin daga banki ne, inda wasu bankunan suka bada uzurin su amma suna kan aikin biyan ma’aikatan.
Ma’aikatan Kaduna sun koka kan rashin biyan su haƙƙin su A jihar Kaduna, bincike ya nuna cewa da yawan ma’aikatan da aka ɗauka a shirin SPW basu samu kuɗaɗen su ba.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan, Jibril, daga ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, yace har yanzun ba’a biya shi ko sisi ba.
Yace:
“Mafi yawancin mu daga ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa ba’a bamu hakkinmu ba kuma ba mu san dalili ba saboda an kammala aikin tun watan Afrilu.”
Shugaba Buhari ya amince da ɗaukara ma’aikata 774,000 a tsarin SPW.
A shekarar da ta gabata, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da ɗaukar ma’aikata 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma 774 da ake da su a Najeriya.
FG tace tsarin zai ƙunshi mutanen da basu da aikin yi kuma ba su da ƙwarewar sana’a daga ƙananan hukumomi 774.
Sai-dai waɗanda aka ɗauka a tsarin, zasu gudanar da wasu ayyukan gyara a yankunan su kamar tsaftace kan hanya da sauransu.