Bayan Rasa 200k a Gurin Caca: Matashi ya Fadi Sumamme

Wani mutum ya hadu da bacin rana inda ya yi asarar zunzurutun kudi har N200,000 a wajen buga caca.

Mutumin ya yanke jiki ya fadi sumamme a bakin shagon gidan cacan domin dai rancen kudin ya yi kuma gaba daya ya rasa su.

Jama’a a shafukan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu, inda wasu suka dunga zolayar mutumin.

Wani mutumi ya yanke jiki ya fadi sumamme bayan ya ari makudan kudade don buga caca.

An tattaro cewa mutumin ya ari kudi N200,000 sannan ya yi amfani da shi wajen buga caca, amma abun bakin ciki sai ya sha kaye inda ya rasa komai.

Wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno mutumin kwance magashiyan a kasa a kofar shagon buga cacan bayan asarar da ya yi.

Karanta martanin mutane a kasa

gabrielpeter805 ya rubuta:

“Wa ya kara wannan wakar, kwata kwata wannan mutumin ba zai ji kamshin lahira ba balle har ya shiga.”

jamoblaq77 ya ce:

“Zai tashi anjima ku kyale shi watakila ya zata mafarki yake yi”

__h.o.I.u.w.a_s.e.u.n_ ya ce:

“Su mayar mai da 50k don ya sake buga wani”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here