Shehun Borno ya Roƙi Shugaban Hafsan Sojoji Akan ya Taimaka ya Maida Manoma Yankunan su

 

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Elkanemi, ya yi kira ga sabon hafsan sojoji ya maida hankali kan wasu wurare a Borno.

Sarkin yace yanzun an samu zaman lafiya a jahar idan ka kwatanta da wasu loƙuta kafin shekarar 2015.

Ya kuma roƙi sabon COAS ɗin da ya taimaka ya maida manoma yankunan su sabida mutanen Borno Manoma ne.

Mai martaba shehun Borno, Alhaji Abubakar Elkanemi, ya roƙi sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo janar Farouk Yahaya, da ya ƙara maida hankali kan wasu wurare da har yanzun ba’a iya zuwa saboda ayyukan yan ta’addan Boko Haram, kamar yadda premiun times ta ruwaito.

Basaraken yayi wannan kira ne ranar Jumu’a da yamma yayin da ya karɓi baƙuncin sabon COAS a fadarsa dake Maiduguri.

Sarkin yace duk da cigaban da aka samu a yaƙin da ake da masu tada ƙayar baya daga 2015 zuwa yau, amma har yanzin akwai wuraren da ba’a iya zuwa saboda yawaitar hare-haren yan ta’adda.

Yace a halin yanzun babu wata ƙaramar hukuma dake hannun yan ta’addan, ba kamar baya ba kafin 2015, lokacin da ƙananan hukumomi 17 ke ƙarkashin ikon su.

Yace: “Mun sha wahala sosai a hannun yan ta’adda idan ka kwatanta da zaman lafiyan da muka samu yanzun.”

“Akwai wani lokaci da bamu da sabis ɗin waya, filayen jirgin mu basa aiki, ba tsaro a dukkan hanyoyin mu in banda hanyar Maiduguri zuwa Kano, kuma an kashe mutanen mu da dama harda masu riƙe da sarautar gargajiya.”

“Kafin 2015, kimanin ƙananan hukumomi 17 ne ke hannun yan ta’addan Boko Haram, amma yanzun duk sun dawo karƙashin kulawar jami’an soji.”

Shehun Borno ya roƙi COAS ya taimaka manoma su koma sana’arsu

Alhaji Elkanemi ya bayyana cewa mutane na jin tsoron komawa wasu daga cikin ƙauyukan su.

Yace: “Muna roƙon shugaban rundunar sojin ƙasa yayi amfani da duk wata dama da yake da ita, ya taimaka wa manoma su koma gonakinsu, saboda mafi yawan mutanen Borno manoma ne.”

“Wurare kamar Baga, Krenoa, Marte, Gamboru-Ngala, waɗanda suke da iyaka da tafkin Chadi, sune inda mafi yawan mutanen wurin manoma ne da masu kamun kifi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here