Tsarin da Muka Fitar Don Tallafawa Yaran da Basa Zuwa Makaranta – Dr. Umar Buba Bindir

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa Najeriya ta shige gaba, wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta a faɗin Najeriya, da adadin yara miliyan 13 da ke zaune a gida, ko suke gararamba a gari.

Bayan waɗannan alƙaluma na MDD tuni gwamnatin Najeriyar ta ce ta fara wani bincike domin kididdige yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

A cewar Shugaban shirin tallafa wa masu karamin karfi na kasar, wato National Social Investment Programme da ma’aikatar ayyukan jin kai ke gundanarwa, kawo yanzu an gudanar da aikin kidayar yaran a wasu jihohi.

Dr. Umar Buba Bindir, ya shaida wa BBC cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya kadu sosai a lokacin da ya ji alkaluman da aka fitar na yaran da su zuwa makaranta ya.

”Wannan dalili ne ya sa aka zauna aka yi nazari sosai saboda muhimmancin da ilimi ke da shi a cikin al’umma” in ji Dr bindir.

Ya ce,” Ba tare da bata lokaci ba shugaba Buhari ya bayar da umurnin a dauki matakin da ya dace wajen magance wannan matsala, inda ya ce me zai hana a gina makarantu a kusa da inda yaran suke, ta yadda ba za su rinka shan wahala wajen neman ilimin ba”

Ya ƙara da cewa ”Akwai hukumar kididdiga ta kasa tana nan tana bin garuruwa da kauyuka domin tantance yaran da ba su zuwa makaranta – in ji shugaban National Social Investment Programme.

Dr. Umar Buba Bindir, ya ce wannan matsala ta rashin zuwan yara makaranta ba arewacin Najeriya kadai ta shafa ba, ba in da babu inda ba ta shafa ba, saboda binciken da suke yi ya nuna hakan.

Ya ce, “A yanzu mun shirya nan da wata daya zuwa wata biyu cewa in sha Allah za a fara koya wa irin wadannan yara abubuwa hudu, wato turanci da lissafi da yadda za a zauna lafiya da kuma sana’a”.

”Sannan za mu rinka ciyar da su abinci sau uku (a rana), kuma an samar da malamai wadanda za su yi ta koya musu abubuwa tun safe har zuwa dare a kowacce rana”, in ji shi.

Ya ce, iyalan yaran kuma idan an gano su za a sanya su kan tsarin nan na basu naira dubu biyar a kowanne wata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here