Gwamna Tambuwal ya Jaddada Goyon Bayan sa ga Rundunar Sojin Ƙasa Domin Magance Rashin Tsaro

 

Gwamnan jahar Sokoto, Mai girma Aminu Waziri Tambuwal ya jaddada goyon bayan sa ga rundunar sojin ƙasan Najeriya domin magance matsalar rashin tsaro da ke damun arewa maso yamma.

Gwamnan ya yi wannan alwashi ne a yayin da yake ƙarɓar babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya a gidan gwamnati da ke Sokoto.

Babban hafsan ya kai wannan ziyarar aikin ne domin samar da mafita da duba shirin runduna ta 8 na kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Gwamna Tambuwal wadda ya bayyana cewa ziyarar babban hafsan, ziyara ce ta ɗan gida, wato mahaifar sa ta jahar Sokoto.

Ya yi kira ga babban hafsan da ya sake fasalin ayyukan rundunar domin magance ayyukan ƴan ta’adda.

Ya kuma yi tir da kuma nuna juyayin abin da ya faru a garin Goronƴo.

Gwamnan ya yi kira da samar da haɗin kai domin bayyanar da masu ɓarna a tsakanin al’umma.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ƙarin dakaru domin samun sauƙin ayyukan rundunar.

A jawabin sa tun da farko, babban hafsan sojin ƙasan, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya yabawa gwamna Tambuwal domin bayar da goyon baya ga ayyukan rundunar a jahar.

Ya yi alƙawarin ci gaba da taimakawa rundunar domin samun zaman lafiya a jahar.

Ya ƙara da cewa rundunar na aiki da sauran hukumomin tsaro domin samun nasarar ayyuka a yankin.

A yayin ziyarar sa a shelkwatar runduna ta 8, babban hafsan ya saurari jawabi daga bakin kwamandan rundunar, Manjo Janar Uwem Bassey a kan gudanar da ayyukan rundunar.

Janar Yahaya ya yabawa hafsoshi da ƙananan sojojin rundunar domin jajircewar su wajen gudanar da aiki.

Ya ce zai tabbatar da samar ma su da dukkan kayan aiki domin gudanar da ayyukan su.

Babban hafsan ya kuma yi alƙawarin gina sababbin ɗakunan kwana a barikin da kuma samar da dukkan kayayyakin aiki domin amfanin dakarun.

A ci gaban babban hafsan na kyautatawa dakarun domin ƙarfafa masu gwiwa, ya miƙa makullin mota ƙirar Toyota Hilux ga babban sajan rundunar ta 8 domin sauƙaƙa masa wajen gudanar da aikin sa a matsayin sa na jagoran ƙananan sojoji.

Babban hafsan ya kuma kai ziyarar ban girma ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III inda ya nemi goyon baya da haɗin kan sarakunan gargajiya domin yaƙi da ta’addanci a yankin.

A jawabin sa, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga babban hafsan da ya yi duk abin da zai iya domin kawo karshen ɓarnan ƴan ta’adda a jahar.

Ya kuma yi alƙawarin gaggauta bada dukkan goyon baya domin samun nasarar rundunar.

Daga nan, babban hafsan ya ziyarci sansanin rundunar da ke yankin Sabon Birni da Isa inda ya yi kira ga dakarun da su zauna a cikin shiri domin gujewa harin bazata.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojojin Ƙasan Najeriya
18 OKTOBA 2021

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here