Jiga-Jigan Jam’iyyar APC na Jahar Taraba da ke Hangen Kujerar Ministan Wuta

Jagororin APC na Taraba suna sha’awar rike mukamin Ministan wuta.

Shugaban jam’iyyar na Taraba yace mutane har 32 suke harin kujerar.

Daga ciki akwai Garba Umar, Sani Danladi da Sanata Yusuf Abubakar.

Taraba – Akalla jagororin jam’iyyar APC 32 a jahar Taraba suna neman maye gurbin Saleh Mamman, wanda aka tsige daga mukamin Ministan wuta.

Jaridar Daily Trust tace manyan ‘yan siyasan Kano da Taraba inda Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman suka fito, suna hangen kujerun Ministocin tarayya.

Ana sa rai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sunayen wadanda za su maye guraben Ministocin da ya kora da zarar ‘yan majalisa sun dawo aiki.

Shugaban APC na Taraba, Barista Ibrahim El-Sudi yace ‘ya ‘yan jam’iyyar 32 suke son wannan kujera.

Su wanene ke neman Minista?

El-Sudi bai ambaci sunayen masu sha’awar kujerar ba, yace babu wanda ya tuntubi jam’iyyar domin kamun kafa, amma yace ya kamata a bar ta a jahar.

Wadanda ake gani sun kwallafa ransu wajen zama Minista a gwamnatin Buhari sun kunshi tsofaffin gwamnoni, Sanata, Jakadu da kuma kwamishinoni.

Tsofaffin gwamnonin rikon kwarya da aka yi a jahar; Alhaji Garba Umar da Sani Danladi Abubakar suna cikin wadanda suke sa ran samun mukamin.

Haka zalika akwai Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, tsohon Jakadan Najeriya zuwa kasar Trinidad and Tobago, Alhaji Hassan Jika Ardo da kuma Cif David Kente.

Rahoton yace shi ma tsohon kwamishinan tattali na jihar Taraba, Alhaji Ahmed Yusuf, yana neman kujerar. Yusuf ya taba neman takarar gwamna a baya.

Wasu masu neman zama Ministocin sun tattara sun koma birnin tarayya Abuja, sun tafi fadar shugaban kasa domin su nemi alfarmar masu madafan iko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here