Har Yanzu Muna Tattaunawa Kan Batun Karin Farashin Man Fetur – Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin tarayya ta ce babu ranar kara farashin litan man fetur.

Mai magana da yawun karamin ministan mai ya jaddada hakan Gwamnoni a baya sun bukaci a kara farashin zuwa N380 ga lita.

Watanni uku bayan gwanonin Najeriya sun bukaci gwamnati tarayya ta kara farashin man fetur zuwa N380, gwamnati ta jaddada cewa har yanzu tana tattaunawa da yan kwadago.

Gwamnati ta jaddada cewa har yanzu bata kammala tattaunawa da yan kwadago ba saboda haka ba za’a kara kudin ba.

Garba Deen Muhammad, mai magana da yawun ministan man fetur, Temipre Sylva, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a.

Garba ya ce zai sake jaddada matsayar maigidansa wanda shine matsayar gwamnatin tarayya.

Garba yace yace mutane da yan kasuwarn mai su cigaba da maganganunsu yadda suka ga dama amma gwamnati ba zata canza kudin mai ba yanzu.

Yace:

“Gaskiyar lamarin shine babbar abinda zai sa mu yanke wani shawara shine idan mun cima matsaya da kwadago. Saboda haka duk abinda gwamnoni ko wani zai fasa, kungiyar kwadago saurara.”

“Har yanzu muna tattaunawa da kungiyar kwadago. Ba zamu yanke wani shawara ba har sai an gama tattaunawa.

Saboda haka kowa ya fadi abinda ya ga dama.” Yayinda aka tambayesa lokacin da za’a gama tattaunawa da kwadago, Garba Deen ya ce gwamnatin tarayya bata yanke ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here