Tinubu: Jagoran Jam’iyyar APC Ya Yanke Jiki ya Fadi a Arewa House

 

Wani bidiyo da ke nuna lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya yanke jiki ya fadi ya janyo cece-kuce tsakanin yan Nigeria.

Jagoran na kasa na jam’iyyar APC ya fadi ne a wurin taron shekara-shekara karo na 11 na Arewa House da ake yi yau a Kaduna.

Wasu sun ce tsautsayi ne da zai iya faruwa da kowa yayin da wasu kuma suke ganin wani abu da ya dace a zurfafa bincike Wani faifan bidiyo da ya fito da ke nuna jagoran jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa ya yi yanke jiki ya fadi ya janyo maganganu tsakanin yan Nigeria.

Tsohon gwamnan na jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya yanke jiki ya fadi yayin taron Arewa House karo na 11 da aka yi a dakin taro na Banquet da ke Kaduna.
A bidiyon da wani mai amfani da Twitter @emmaikumeh ya wallafa, Tinubu, wanda shine shugaban taron ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke kokarin tafiya tsakanin wasu kujeru da masu tsaronsa a tare da shi.

Ba a tabbatar da abinda ya yi sanadin faduwarsa ba amma nan take masu tsaronsa sun taimaka sun daga shi da suka gano abinda ke faruwa.

Bidiyon ya janyo cece-kuce tsakanin yan Nigeria a Twitter.

Wasu na cewa wannan ba wani abu bane domin zai iya faruwa da kowa yayin da wasu ke ganin kamar alama ce da ke nuna ba shi da lafiya kuma ya kamata a duba batun musamman saboda hasashen da ake yi na cewa zai yi takarar shugaban kasa a 2023.

@PreciousAmurika ta ce:

“Mutumin da ke fadi kamar tsohuwar fanka na tsaye yana son ya zama shugaban kasa tamkar mataccen katakon da muke da shi a yau.”

@macfriet ta ce

“Ina ganin kawai ya taka babban rigarsa ne yayin da ya ke tafiya, kada ku yi saurin yanke hukuncin, Idan da fadi ya yi bai tashi ba, da an garzaya da shi asibiti.
Amma ya tsaya ya gabatar da kasidarsa.”

@uchebakaadi ya ce:

“Akwai yiwuwar Alhaji ya yi karo da wani abu a wurin taron nan. Wancan ranar hannunsa na rawar kamar DJ Jimmy Jatt a wurin taro. Watakila lokaci ya yi da zai yi murabus ya koma gida ya huta da yaransa da matarsa. Akwai yiwuwar Asiwaju bai fadi ba. Allah ba zai kunyata mu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here