Shugaba Tinubu ya Gana da Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu

 

FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa yanzu haka da tsohon ministan ilimi da ya gabata, Adamu Adamu, a fadar shugaban ƙasa Aso Rock, Abuja.

Mista Adamu ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 1:30 na rana yau Talata, 4 ga watan Yuli, 2023 kuma daga isarsa ya shiga taron sirri da Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ba bu wani cikakken bayani kan maƙasudin wannan ganawa ko kuma muhimman batutun da zasu tattauna a taron.

Sai dai duk da ba’a bayyana ajendojin wannan zama ba amma taron ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin Ministocin da shugaban ƙasan ke shirin tura wa majalisa.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here