Tinubu Zai yi wa Majalisar Ministoci Kwaskwarima nan Gaba Kaɗan – Onanuga

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa zai yi wa majalisar ministocinsa kwaskwarima nan gaba kaɗan, a cewar mai magana da yawunsa Bayo Onanuga.

“Shugaban ƙasa ya ce zai yi wa majalisarsa kwaskwarima. Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi […] bai faɗa mana lokaci ba dai” in ji shi lokacin da yake magana da manema labarai a yau Laraba.

Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministcin “da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai” domin tallata ayyukan gwamnatin.

A cewarsa: “Wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi.”

Babu tabbas game da dalilin da ya sa Tinubun zai yi sauyin a daidai wannan lokaci. Akasarin ministocin gwamnatin Muhammadu Buhari – wanda Tinubu ya gada – sun shafe kusan shekara takwas a kan mulki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here