Shugaba Tinubu ya Nada Mai Shekaru 32 a Matsayin Sabon Shugaban NASENI

 

Shugabancin Dr. Bashir Gwandu a hukumar NASENI ya zo karshe daga Satumban nan na 2023.

Bola Ahmed Tinubu ya dauko Khalil Suleiman Halilu a matsayin sabon shugaban hukumar kasar.

Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar nada ‘dan shekara 32 da haihuwa da yawun shugaban kasa.

Bola Ahmed Tinubu ya sallami Dr. Bashir Gwandu daga kujerar da ya ke kai ta babban shugaban hukumar nan ta NASENI.

Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale, ya sanar da haka a yammacin Juma’a.

Ajuri Ngelale ya ce wanda zai maye gurbin Gwandu a NASENI shi ne Khalil Suleiman Halilu.

Gwamnatin tarayya ta kafa wannan hukumar ne domin kula da kimiyya a bangaren samar da abubuwan more rayuwa a Najeriya.

Khalil Suleiman Halilu Kamar yadda jawabi ya fito daga fadar shugaban Najeriya dazu, Khalil Suleiman Halilu zai yi shekara biyar a kan mukamin.

Kamar yadda dokokin NASENI na 2014 su ka yi tanadi, sabon shugaban zai iya zarcewa kan kujerar bayan wa’adin farko ya kare.

Da wannan nadin mukami da aka fitar a ranar 1 ga Satumban 2023, wa’adin Khalil Halilu mai shekara 32 zai kare ne a 2028.

Cif Ngelale ya ce ana sa ran sabon shugaban hukumar ya yi amfani da kwarewarsa wajen kawo cigaba a hukumar tarayyar.

Matashi ya samu shiga

Makonni bayan nada ministoci, da wannan umarni na shugaban kasa, nadin mukamin ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Watakila Mista Khalil shi ne mai mafi karancin shekaru a wadanda Bola Ahmed Tinubu ya ba mukami bayan hawansa kan mulki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com