Bayan Gana wa da Buhari: Tinubu ya Nufi Zuwa ƙasar Faransa
Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa don cigaba da neman shawari bayan gana wa da Buhari.
Mai magana da yawun jigon APC na ƙasa, Tunde Rahman, ya ce Tinubu zai halarci wasu taruka masu muhimmanci a birnin Faransa.
An bayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC bayan lashe zaɓen fidda gwani.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressive Congress wato APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fice daga Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jagoran APC na ƙasa ya nufi ƙasar Faransa bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa Aso Villa dake birnin tarayya Abuja, da safiyar Litinin.
Read Also:
Mai magana da yawun ɗan takarar na APC, Tunde Rahman, wanda ya sanar da lamarin, bai bayyana adadin lokacin da Bola Tinubu zai kwashe yayin tafiyar ba.
Amma a sanarwan, Rahman ya tabbatar da cewa ana tsammanin Bola Tinubu zai dawo gida Najeriya nan ba da jimawa ba.
Ya ce:
“Ya tafi birnin Farisa na ƙasar Faransa domin halartar wasu taruka masu matuƙar muhimmanci.”
Leadership ta rahoto cewa kwana ɗaya kafin tafiyarsa, Tinubu, ya halarci kaddamar da wani littafi mai suna, “Mista Kakakin majalisa,” da buɗe shirin ba da horo kan ayyukan majalisar dokoki duk a wani ɓangare na bikin cika shekara 60 na kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
A ranar 8 ga watan Yuni, aka ayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2023 da ke tafe bayan samun nasara a babban taron zaɓem fidda gwani na jam’iyyar wanda ya gudana a Eagle Square.
Bayan kammala zaɓen, tsohon gwamnan jihar Legas ya kai ziyarar godiya da kuma neman sulhu ga sauran yan takarar da suka fafata da shi ciki har da waɗanda suka janye masa.