Shugaba Tinubu ya yi Sababbin Naɗa-Naɗa

 

Abuja – Kwana biyu bayan rasa wasu masu mukamai a gwamnatinsa, Bola Tinubu ya yi sababbin nade-nade.

Shugaban Tinubu ya amince da nadin Dalhatu Abubakar a matsayin shugaban hukumar kula da kasuwancin kasa, NCX.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da aka wallafa a shafinta na X, an ce sake fasalin kwamitin ya yi daidai da manufofin sabuwar fata da ke mayar da hankali kan wadatar abinci.

Dan Arewa ya samu muƙamin shugaban CAC

Hakan ya biyo bayan nadin da Bola Tinubu ya yi na Sanata Ibrahim Ida a ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.

Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC) wanda ake da ran zai inganta hukumar.

Tinubu ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin wanda zai shugabanci hukumar CAC domin inganta harkokin kasuwanci.

An nada Dalhatu shugaban hukumar NCE

Nadin ya fara aiki nan take, kuma wani bangare ne na kokarin gwamnati na karfafa tsarin kasuwancin kayayyaki da bunkasa fitar da kayayyakin noma zuwa kasashen waje.

Sanarwar ta ce nadin zai taimaka wajen inganta gano farashi, kara gaskiya a kasuwa, da fadada damar fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duniya.

Sababbin mambobin kwamitin sun hada da Najah Muhammed, Bamidele Hussein, Mezuo Nwuneli, Obi Igwe, Foluso Ayo-Olaiya, da Anthony Atuche a matsayin manajan darakta.

Aikin da sabon kwamitin zai yi

Fadar shugaban kasa ta ce sabon kwamitin zai samar da jagoranci mai kyau domin cikakken farfado da cibiyar da kuma jawo masu zuba jari.

Za a mayar da hankali kan bangarorin ajiya, sufuri, da gine-ginen kasuwanci domin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.

Gwamnati ta ce wannan cibiyar na da muhimmanci wajen cimma manufofin wadatar abinci da rage dogaro da man fetur a tattalin arziki.

Ta hanyar tsarin kasuwanci mai kyau da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, za a inganta bin diddigin kayayyaki da daidaita kasuwanni.

Dalhatu Abubakar dan kasuwa ne daga Kano, kuma shugaban kamfanin Al-Hamsad Integrated Rice Mills tare da jagorantar CONSCCIMA a baya.

An kuma bayyana shi a matsayin tsohon shugaban KACCIMA, wanda ya taka rawar gani wajen bunkasa harkokin noma da horar da ‘yan kasuwa a Arewacin Najeriya.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here