Ya Kamata Sabon Shugaban ƙasa ya Tunasar da Mutane Kafin Sanar da Cire Tallafin Mai – Shekarau

 

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce da ya kamata sabon shugaban ƙasar ya yi wa ‘yan ƙasar bayani kafin cire tallafin mai.

Yana mai cewa ya kamata shugaban ƙasar ya bi matakai kafin sanar da cire tallafin kai-tseye kamar yadda shugaban ya yi a jawabinsa na farko bayan shan ranstuwar kama aiki.

”Ya kamata ya sanar da mutane cewa maganar cire tallafin man fetur tun kafin ya zo an yi ta fiye da shekara guda, har ma an cire shi a kasafin kuɗi na shekarar 2023 da muke ciki”, in ji Shekarau

A cikin shirimu na Gane Mini Hanya na wannan makon Mallam Ibrahim Shekarau ya taɓo batutuwa da dama ciki har da batun siyasar jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here