Gwamnatin Togo ta Saka Dokar Ta-ɓa-ci a Arewacin ƙasar

 

Gwamnatin Togo ta saka dokar ta-ɓa-ci kan tsaro a yankin kan iyakarta ta arewacin ƙasar.

Dokar za ta shafe wata uku tana aiki kuma ana sa ran majalisar tarayyar ƙasar za ta ƙara wa’adin dokar, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana.

Wannan matakin zai bayar da dama ga jami’an tsaro su yi aiki tuƙuru don su yaƙi masu iƙirarin jihadi.

Haka kuma wannan na zuwa ne bayan harin da aka kai wani gari da ke arewacin ƙasar kusa da iyaka da Burkina Faso inda aka kashe ƴan ƙasar Togo takwas aka kuma raunata sauran.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here