Gwamnatina Zata ɗau Tsattsauran Mataki Kan ‘Yan Bindigan da Suka Addabi Jahata da Masu ɗaukar Nauyin su – Gwamna Matawalle

 

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, yace zai ɗauki matakin da ya dace a kan yan bindigan da suka addabi mutane.

Gwamnan ya bayyana cewa da farko ya ɗauki matakin sulhu kuma an samu nasara, amma yanzun za’a musu abinda suke so.

Matawalle ya faɗi haka ne a wani jawabi da yayi wa al’ummar jahar bayan wasu munanan hare-hare da aka kai kwanan nan.

Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara, yace gwamnatinsa zata ɗau tsattsauran mataki kan yan bindigan da suka addabi jahar da masu ɗaukar nauyin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka a wani jawabi da yayi ga al’ummar jihar a Gusau ranar Asabar, bayan yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a jahar.

Legit.ng hausa ta ruwaito cewa wasu ɗaruruwan yan bindiga akan mashin sun kai hari ƙauyen Kadawa, ƙaramar hukumar Zaurmi, inda suka kashe mutane da dama, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya sake jaddada ƙudirinsa na ɗaukar mataki kan duk wani mai hannu a hare-haren da ake kaiwa jahar a baya da kuma yanzu.

Yace:

“A yan makwannin nan, aikin ta’addanci ya ɗauki wani sabon salo ba kamar farkon zuwan mu kan mulki ba.”

“Waɗannan mutanen suna kashe kowa ba tare da tausayi ba; mata, tsofaffi da ƙananan yara, babu wanda ya tsira a wurin su.”

“Ku shaida ne kan irin namijin kokarin da gwamnatin mu tayi tun farkon zuwanta madafun iko, musamman tattaunawar sulhu da tazo da shi kuma ta samu nasara.”

Matawalle ya ƙara da cewa a halin yanzu wasu bara gurbi sun sake zuwa zasu canza abinda muka gina yayin da matsalar tsaro sai ƙaruwa take a kullum.

“Addu’ata a kullum itace Allah ya tona asirin duk mai hannu akan waɗannan hare-haren.

Ina mai tabbatar muku gwamnatin mu zata cigaba da ƙoƙarin da take da kawar da ayyukan ta’addanci a faɗin jahar mu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here