Tsawa ta yi Sanadiyyar Hallaka Mutane 17 a Kasar Bangaladesh

 

Wata tsawa ta hallaka akalla mutun 17 cikin mahalarta wani shagalin biki ana cikin cashewa.

Lamarin ya faru ne a cikin wani jirgin ruwa dake kusa da tekun Shibganj a kasar Bangaladesh.

Wasu mutum 14 sun jikkata cikinsu harda Ango yayin da ita amarya ba ta samu halartar wurin shagalin bikin nasu ba.

Bangaladesh:- Hukumomi a ƙasar Bangaladesh sun bayyana cewa aƙalla mutum 17 cikin mahalarta wani bikin aure ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wata tsawa mai karfi.

Rahoto ya nuna cewa wasu 14 sun jikkata, cikinsu harda mai gayya wato Ango, sai dai amarya ba ta samu halartar wurin cashewar ba. BBC Hausa ta ruwaito cewa an shirya shagalin bikin ne a cikin wani jirgin ruwa na musamman dake kusa da tekun Shibganj.

Tsawar ta faɗa musu kashi-kashi Tsawar ta afkawa mahalarta bikin ne yayin da suke cikin jirgin ruwan a kan hanyarsu ta zuwa gidan Amarya.

Wasu mutane da suka ga lokacin da lamarin ya faru sun bayyana cewa tsawar ta faɗa wa jirgin ne kashi-kashi.

Wasu shaidun gani da ido suka ce:

“Kashi-kashi na tsawar ne ya afka cikin jirgin da mahaƙarta shagalin bikin suke ciki.”

Legit.ng hausa ta gano cewa wannan ba shi na farko ba, kuma daman tsawa na yawan hallaka mutane a a faɗin kudancin Asiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here