Tsige Damagum: Atiku ya Fara Tuntuɓar NWC
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya goyi bayan shirin tsige muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum.
Bayanai sun nuna cewa Atiku ya fara tuntuɓar ƴan kwamitin gudanarwa (NWC) waɗanda suka fara fafutukar sauke Damagum daga shugabancin jam’iyyar.
Damagum: Gwamnonin PDP sun dare gida biyu
Jaridar Punch ta tattaro cewa shirin tsige Umar Damagum ya raba kawunan gwamnoni 13 na jam’iyyar adawa PDP.
Gwamnoni bakwai karƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi sun haɗa kai, sun matsala lamba kan dole Damgum ya bar muƙaminsa.
Yayin da gwamnoni huɗu karkashin Gwamna Seyi Makinde na Oyo suka nuna gamsuwa da Damagum, sauran gwamnoni biyu kuma sun ce duk inda ta faɗi sha ne, cewar The Nation.
Read Also:
Gwamnonin da suke goyon bayan Damagum ya ci gaba da shugabancin PDP bakinsu ɗaya da ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda alaƙarsa ta yi tsami da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar.
Atiku da Wike dai sun raba gari gabanin babban zaben 2023, inda Wike ya jagoranci gwamnoni biyar na PDP wajen yaƙar takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Atiku ya fara tuntuɓar ƴan kwamitin NWC
Wani babba a NWC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da ƴan jarida, ya tabbatar da cewa Atiku ya tuntuɓi wasu daga cikin masu shirin sauke Damagum.
Ya ce:
“Ba mu kadai ba ne, manyan shugabanni a jam’iyyar da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun tuntuɓi wasu daga cikin mu.”
“Ina tabbatar maku da cewa Atiku ya kira wasu daga cikinmu, ya nuna mana ba mu kadai za mu yi yakin ba, kuma yana goyon bayan neman adalci, gaskiya, da daidaito.
“Ba mu da wata matsala da Damagum, burin mu shi ne mu kare jam’iyyar domin ‘yan Nijeriya su samu mafita a zabe mai zuwa. Ya kamata Damagum ya mutunta dokar jam’iyya, ya sauka daga muƙamin.”