Dalilin da Yasa Jama’iyyar APC Reshen Jahar Enugu ta Tsige Shugaban Jam’iyyar

 

Rikicin APC a jahar Enugu ya ɗauki wani sabon salo ranar Laraba yayin da jami’an yan sanda suka kwace sakateriya.

Babu wani mamba ko jigon jam’iyyar da jami’an sanda suka bari ya shiga ofishin yayin da suke kokarin dawo da doka da oda.

Jam’iyyar ta tsige shugabanta na jahar inda ake zarginshi da zagon kasa da kuma fatali da dokoki.

Enugu – Jami’an hukumar yan sanda sun kwace iko da ofishin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jahar Enugu domin dawo da doka da oda.

PM News ta ruwaito cewa jami’an sun hana shugabannin jam’iyyar da sauran masu faɗa aji shiga ofishin biyo bayan rikicin shugabanci da ya ɓarke a APC reshen jahar.

Mambobin SEC sun tsige shugaban APC

Legit.ng ta ruwaito cewa mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC reshen jahar Enugu sun amince da tsige shugabansu, Dr Ben Nwoye, bayan kaɗa kuri’a.

Kwamitin ya zargi tsohon shugaban Nwoye da rashin ɗa’a da kuma kawo hargitsi da rabuwar kai a cikin jam’iyyar APC.

Kwamitin ya shaidawa manema labarai cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda zagon kasa da kuma fatali da kundin tsarin mulkin APC da shugaban ke yi.

Shugabannin jam’iyyar sun kaɗa kuri’ar tsige shi daga mukamin shugaba tare da maye gurbinsa da mataimakinsa a matsayin shugaba na Riko. Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban rikon kwarya, Prince Gilbert C. Chukwunta, yace:

“Mambobin kwamiti sun haɗu domin ceto jam’iyyar mu daga rugujewa matukar Nwoye ya cigaba da jagorancin jam’iyyar APC a jahar.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here