Bayan Garkuwa: An Tsinci Gawar Sheikh Mushafau Bakare

 

Ana zargin cewa ‘Yan bindiga sun kashe Sheikh Mushafau Bakare a jahar Ogun.

A jiya aka sace Malamin addinin Musuluncin, a yau da safe aka tsinci gawarsa.

Mushafau Bakare shi ne babban Limamin yankin Atiba, ya shahara a Ijebu-Ode.

Ogun – Mashahurin malamin addinin musulunci, kuma babban limamin Atiba da ke garin Ijebu-Ode, jahar Ogun, Sheikh Mushafau Bakare, ya rasu.

A jiya aka sace Sheikh Mushafau Bakare Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021, ta ce an samu gawar Sheikh Mushafau Bakare bayan an yi garkuwa da shi.

A ranar Laraba, ‘yanuwa da abokan arziki suka fito suka sanar da cewa an dauke wannan bajimin malami.

Sa’o’i kadan da aukuwar wannan lamari, sai aka samu labarin da ya fi wannan muni, Punch ta ce an samu gawar limamin a cikin wata sabuwar motarsa.

Jami’an tsaro sun gano gawar Malamin a Ikangba

Rahotanni sun ce an iske gawar ne a katuwar mota kirar ‘Toyota Highlander; a safiyar yau a wajen yankin Ikangba, a karamar hukumar Odogbolu, Ogun.

Majiya ta shaida wa manema labarai cewa jami’an ‘yan sanda na reshen Obalande, ne suka iske Sheikh Mushafau Bakare ba ya motsi yayin da suke nemansa.

‘Yanuwan babban limamin na garin Atiba, sun yi ta kiran lambar wayarsa a lokacin da ake nemansa ruwa-a-jallo, amma ba a dauki wayar salular ba.

‘Yan jarida sun yi kokarin tuntubar kakakin ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, a game da wannan lamari mai ban takaici, amma ba a iya samunsa ba.

Jaridar The Will Nigeria tace har zuwa yanzu da ake kawo wannan rahoto, ‘yan sandan jahar Ogun ba su fitar da jawabi a game da mutuwar malamin ba.

Ana sa ran an birne shehin malamin da safe a unguwarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here