Maguzawa Sune Suka Kafa Kano: Aisha Yesufe ta yi Tsokaci Kan Maganar

 

Aisha Yesufu ta yi tsokaci kan maganan da aka ce ta ce Maguzawa sune suka kafa jahar Kano.

A cewarta mutane basa karatu da fahimta, domin ita cewa tayi akwai Maguzawa ‘yan asalin jahar.

Ta kalubalanci masu sharhi kan lamarin da su koma su karanci tarihi domin jin yadda lamarin yake kan usulin Maguzawa a jahar.

Shahararriyar mai fafutukar nan ta Najeriya, Aisha Yesufu ta yi tsokaci a kan rade-radin da mutane ke yi na cewa ta ce Maguzawa sune suka kafa jahar Kano, lamarin da ya haifar da zafafan martani daga fusatattun mutane.

Kamar yadda muka sani dai Kalmar Maguzawa tana nufin mutane da ke zaune a kasar Hausa amma kuma suke ba Musulmai ba.

Aisha ta jadadda cewa ko shakka babu tarihi ya nuna cewa akwai Maguzawa ‘yan asalin jihar Kano wadanda suke su Kiristoci ne tun a zamanin da.

Sai dai ta ce sabanin yadda aka fadi zancen ita cewa tayi babu inda yake a kasar da za a ce an samu ‘yan asalin wuri guda kuma ace dukkansu addininsu daya.

A hira da Editan Legit.ng Hausa yayi da ita an jiyo tana cewa:

“Zancen da nayi a kan Twitter na cewa Maguzawa sune a Kano, dama su aka sani a wajen, shine abun da ake kira tarihi mutane basa karanta shi ne ko yaya? Wani abu ma da naji ance na fadi shine wai nace kiristoci ne suka kafa jahar Kano, nace toh a ina kiristoci suka kafa ta tunda addinin Musulunci ya zo kafin kiristanci ya zo nan Kanon.

“Abun da na fada, ana zance ne wani ne yayi zance a kan cewa akwai Musulmai da suke Inyamurai kuma asalinsu Inyamurai ne a chan inda Inyamurai suke. Nace gaba daya Najeriyarnan ba inda yake da za ka hadu ace akwai mutanen da suke da asali wai babu wani addinin da ya banbanta da wadanda suke da yawa.

“Sai na kawo misali nace ko a Kano ma akwai Maguzawa da suke su ba Musulmai bane su Kiristoci ne kuma yan Kano ne, kuma sune ma asalin yan Kanon, abun da na fada kenan. Maganar ba haka yake ba? A Kanon akwai su a Jigawa akwai su, babu inda babu su, yawa ne basu da shi kamar yadda sauran suke. Maganar da nayi kenan, toh ban ga me yasa in aka yi abu daya masu juyawa suyi ta juyawa, masu kawo canfe-canfe suyi ta yi ana fadin abubuwan da bai kamata ba.

“Menene a ciki? Magana ne yadda yake kuma an fade shi menene a ciki. Don nace akwai Kiristoci a Kano toh me kenan?

“Ya kamata mutane su dunga karatu da fahimta, shiyasa ko a makaranta lokacin da ake koyon yare, ko Hausa ko Turanci akwai abunda ake kira fahimta, idan ka karanta abu ka fahimci abun da ake nufi ba wai ka karanta don ka bayar da amsa ba. Sannan a cikin wannan yanayin da nayi magana dama ka sa sai na dauko na kalle shi sai na fassara, har sai da nace Kalmar maguzawan wasu suna daukar shi kamar ma kalan zagi ne ma, da na fadi hakan ma sai nace yawancinsu ba Musulmai bane ma Kirista ne, ko suna ganin kamar ba ‘yan Kanon da suke su kirista ne?

“Maguzawan ba sune suke a su Dala da Gauron dutse? Maguzawan ai ba Hausa suke yi ba, kuma ba sune ‘yan asalin Kanon ba? Sannan da Hausawa ai wannan ba wani abun fada bane, a nemi tarihi mana a karanta. Tun ina Sakandare, na fara sakandare a GGSS Kabo tun lokacin akwai ma wata Saratu Musa ‘yar ajinmu ita Bamagujiya ce ‘yar Kano. Mun karanta a tarihi ko kuma suna so su juya tarihi ne, na ga mutane komai suna so su juya shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here