Tuhume-Tuhumen da ake yi wa El-Rufai
Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026.
An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji.
A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta bai da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki, tare da buƙatar samun isasshen lokaci domin shirya kare shi a kotu.
Sai dai ɓangaren masu ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna mai cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Rufai masu nauyi ne, kuma bayar da beli na iya kawo cikas ga binciken da ake ci gaba da yi.
Alƙalin kotun ya ɗage sauraron buƙatar neman beli zuwa ranar 31 ga watan Maris, bayan da mai gabatar da ƙara na ICPC ya ce idan aka bayar da belin tsohon gwamnan to zai iya lalata shari’ar.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu bisa zargin cin hanci da kuma amfani da mukami ba daidai ba.
A ranar Talatar nan ne hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotuna guda biyu duk a Kaduna.
Hukumar ta ce ta gurfanar da shi tare da wani Joel Adoga a Babbar Kotun Tarayya da kuma wani Amadu Sule a wata babbar kotun ta daban duka a
Tun dai ranar 19 ga watan Fabrairu ne tsohon gwamnan jihar ta Kaduna ke riƙe a hannun hukumar ICPC bayan da ta kama shi jim kaɗan bayan sakin sa da hukumar EFCC ta saske shi.
A ranar 5 ga watan Maris ne wata kotun majistire ta bai wa ICPC damar tsawaita tsare El Rufai da mako biyu.
Da me ICPC ke tuhumar El Rufai?
Read Also:
A wata sanarwar da ICPC ta fitar a ranar Litinin kan gurfanar da shi a gaban kuliya, hukumar na tuhumar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da zarge-zarge da dama da suka haɗa da:
Karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida.
Mallakar kadarorin jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Halasta kuɗaɗen haram.
Hukumar ta ICPC ta ce an shigar da karar ne domin a bi diddigin zargin da ake yi.
Haka kuma, ICPC ta bayyana cewa akwai wata ƙara ta daban da aka shigar a Babbar Kotun Jihar wadda ta shafi El-Rufai da wani Amadu Sule.
A cikin wannan ƙarar, ana zargin su da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba da damfara, yunƙurin aikata damfara, da kuma fifita wasu ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta ce an shigar da duka ƙararrakin biyu ne a ranar 18 ga Maris, 2026, kuma an riga an miƙa wa El-Rufai sammaci yadda ya kamata.
El Rufai da hukumar DSS
Malam Nasir El Rufai yana fuskantar wata shari’ar da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS kan zargin sauraron wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Babbar kotun Abuja ta fitar da ranar 23 ga watan Afrilu domin gurfanar da El Rufa’i a gabanta kan tuhumar.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya musanta zarge-zargen da aka yi masa ciki har da binciken da hukumar ICPC ta gudanar a gidansa wanda ya bayyana da “haramtacce”.
Ya kuma shigar da ƙara inda yake neman naira biliyan ɗaya daga wurin ICPC da Sifeto Janar na ƴansanda tare da buƙatar soke sammacin da aka yi amfani da shi a kansa da kuma hana hukumomi dogara na binciken da aka yi a gidansa.
Sai dai kuma hukumar ICPC da rundunar ƴansanda su ma sun nemi kotu ta yi watsi da ƙarar, inda suka ce binciken da aka yi a gidansa halastacce ne wanda aka samu daga kotun da ke da hurumin yin hakan.















