Da Zarar Twitter ta yi Rijista da NBC da CAC Zamu Janye Dakatarwar – Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce bata hana yan kasa amfani da Manhajar Twitter ba.

Gwamnatin ta ce duk da dakatarwar, yan Nigeria na cigaba da shiga Twitter da VPN.

Gwamnatin ta ce za ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter da zarar ta yi rajista da NBC da CAC.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta fada wa babban kotun tarayya a Legas cewa bata hana yan Nigeria amfani da dandalin sada zumunta na Twitter ba, tana mai cewa har yanzu yan Nigeria da dama suna amfani da shi a kullum, rahoton The Punch.

Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami, da gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne yayin bada amsa kan wani kara da lauya mai rajjin kare hakkin bil adama, Inihebe Effiong ya shigar game da batun na hana amfani da Twitter.

A ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin Nigeria ta dakatar da ayyukan Twitter kimanin kwanaki biyu bayan Twitter ta goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a dandalin.

Sai dai, yan Nigeria da dama na amfani da manhajar VPN mai badda-kama domin amfani da manhajar na Twitter duk da dakatarwar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Malami, ciki wata sanarwa da ya fitar ya yi barazanar tuhumar yan Nigeria da ke cigaba da amfani da manhajar yayin da NBC ta umurci dukkan gidajen rediyo da talabijin su dena daukan labarai daga Twitter.

Lauyan mai rajjin kare hakkin bil adama, Effiong, ya yi karar Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Malami, da gwamnatin tarayya bisa dakatar da Twitter.

A cikin karar Effiong ya nemi kotu ta hana gwamnati dakatar da amfani da manhajar ko hana mutane amfani da wasu dandalin sada zumuntar da wasu bukatu takwas da ya ce keta hakkin bil adama ne.

Dakatar da Twitter ta take hakkin bil adama bane Sai dai, Mr Ilop Lawrece a madadin gwamnatin tarayya da AGF ya ce dakatar da Twitter ba take hakkin bil adama bane domin har yanzu yan Nigeria na cigaba da amfani da Twitter.

Ya kuma ce yan Nigeria na da damar bayyana ra’ayoyinsu da sukar gwamnati idan bukatar hakan ya tashi a wasu kafafen kamar WhatsApp, Facebook, Tiktok da wasu sauran.

Gwamnatin tarayyar ta kuma ce yan Nigeria su dena fushi da ita domin ba laifinta bane domin Twitter ta ki bin dokokin kasa.

Gwamnatin ta fadawa kotu cewa za ta janye dakatarwa da ta yi wa Twitter da zarar kamfanin ta yi rajista da NBC da CAC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here