Ukraine ta kai wa Rasha Hari
Wani hari da Ukraine ta kai ta amfani da jirgin mara matuƙi ya haddasa gobara a wata babbar tashar jiragen ruwa da ke Tekun Baltic a arewa maso yammacin Rasha.
Gwamnan yankin Leningrad ya ce ana ƙoƙarin shawo kan gobarar da ta tashi a tashar Ust-Luga,, yana mai ƙara da cewa ba a samu rahoton asarar rai ba.
Read Also:
Tashar na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin fitar da kayayyakin Rasha zuwa ƙasashen waje, ciki har da taki, da man fetur da kwal.
A ranar Litinin, Ukraine ta kai wani hari makamancin wannan wanda ya haddasa gobara a tashar Primorsk Port, wadda ita ma ke kusa da iyakar Finland a arewa maso yammacin Rasha.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya zargi Rasha da nuna “mugunta matuƙa” bayan da ta kai daya daga cikin munanen hare harenta a ranar Litinin. Rahotanni sun ce Rasha ta harba kusan jiragen yaƙi marasa matuƙi dubu guda cikin sa’o’i 24.















