Warin Jiki: An Fatattaki Fasinjan Jirgin Sama da Iyalinsa

 

An bukaci wani fasinjan jirgin sama, Yossi Adler, matarsa, Jennie da diyarsu su fita daga wani jirgi bayan sauran fasinjoji sun yi korafi.

An rahoto cewa an yi zargi mutumin da iyalinsa suna warin jiki wanda ya jefa sauran mutane cikin wani hali.

Mutumin ya nuna fushinsa, cewa fasinjojin da jirgin na Amurka sun ci zarafinsa da iyalinsa.

Wani mutumi mai suna Yossi Adler, matarsa Jennie da diyarsu sun shiga wani jirgin sama amma sai aka fatattake su bayan sauran fasinjoji sun yi korafin cewa suna mugun wari.

Mutumin ya koka cewa kamfanin jirgin bai yi masa da iyalinsa adalci ba kuma basu samu yin tafiyar yadda suka tsara ba.

Dalilin da yasa kamfanin jirgin Amurka ya fatattaki wani mutum da iyalinsa daga jirgi Ya bayyana cewa an nuna musu wariya saboda addininsu don su Yahudawa ne, rahoton Daily Mirror.

WPLG Local 10 News ta nakalto yana cewa:

“Akwai wani dalili na addini da ya sa suka kore ni daga cikin jirgi, ba ma wari. Babu wanda ke da wari a nan, kwatsam, muna tashi, sai suka rufe kofar sai suka ce ka yi hakuri yallabai, wasu sun yi korafi cewa kana da warin jiki don haka ba za mu bari ka koma ba.”

Kamfanin jirgin Amurka ya tabbatar da cewa an fatattaki ma’auratan da diyarsu daga jirgin amma sun ce an yi masu hayar wani jirgin. Kamfanin jirgin ya ce an tarairaye su da kyau sannan an basu tikitin abinci.

“An cire Mista Adler da matarsa daga jirgin sama lokacin da fasinjoji da dama suka yi korafi a kan warin jikinsu. An kama masu daki a otel don su kwana sannan an basu tikitin abinci. An sake kama masu wani jirgin a ranar Alhamis.”

Ma’auratan sun ce sun fito daga jirgin sannan sun tambayi sauran mutane a filin jirgin ko da gaske suna wari.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com