Allah ya maimaita Mana irin Buhari a 2023: Gwamna Wike ya yi Martani Kan Addu’ar Gwamna Umahi

 

Gwamnan Rivers ya yi martani mai zafi ga gwamnan Ebonyi kan addu’an da yayi.

Umahi yayi addu’an cewa Allah ya maimaita mana Buhari a 2023.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamna Umahi ranar Litinin.

Gwamnan jahar Rivers, Nyesom Wike, a ranar Laraba ya caccaki takwararsa na jahar Ebonyi, Dave Umahi, wanda yace Allah ya Najeriya shugaba irin buhari a 2023.

Umahi a ranar Litinin yayinda ya kaiwa Buhari ziyara fadar shugaban kasa, yayi addu’an Allah ya maimaitawa Najeriya mutum mai kirki irin Buhari a 2023.

Amma ranar Laraba, Wike yayi raddi mai zafi ga Dave Umahi inda yace ko shugaba Buhari ya san Allah ba zai ba Najeriya shugaba irinsa a 2023 ba, rahoton Punch.

Yace:

“Haka wani gwamna ke cewa yana addu’a Allah ya maimata mana irin Buhari.”

“Sai nace wai me matsalar shi ne? Shin baku ganin akwai bukatar duba kwakwalwarsa? Jahilci kawai.”

“Kuma ka san Shugaban kasa ya san karya kake masa. Shi (Buharin) ya sani. Abin dai akwai takaici. Allah ya iya mana.”

Wike ya yi Alla-wadai da irin rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta karkashin Buhari da kuma rashin adalcin dake faruwa.

Gwamnan yayi maganan ne a taron masu ruwa da tsaki a birnin jahar Fatakwal inda yake jawabi ga yan kasuwa kan rikici kudin harajin da yake da hukumar FIRS.

Wike da Umahi sun dade suna ja’inja tun lokacin da gwamnan na Ebonyi ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP.

Me Dave Umahi ya fadi? Dave Umahi, ya bayyana fatan wanda ke da “kyakkyawar zuciya” kamar Shugaba Muhammadu Buhari zai fito a matsayin wanda zai maye gurbinsa a 2023.

Ya fadi hakan ne duk da cewar ya ce ya yi wuri sosai da za a shiga harkokin siyasar 2023 kamar yadda ya lura cewa hakan zai zama shagala a bangaren shugaban kasa da gwamnonin jahohi.

Ya kuma kara da cewa membobin jam’iyyun siyasa daban-daban daga Kudu maso Gabas suna aiki a cikin jam’iyyunsu don tabbatar da ganin cewa an mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here