Sababbin Wuraren da Korarrun ‘Yan Bindigar Zamfara Suka Koma

 

‘Yan bindigar da suka addabi al’umma a jahar Zamfara na ci gaba da tserewa tun bayan da gwamnati ta dauki matakan tsaro masu tsauri a kansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa a yanzu yan bindigar na tserewa yankunan Kebbe da Lambar Tureta a jahar Sokoto da kuma Birnin-Gwari a Kaduna.

An tattaro cewa luguden wutan da dakarun sojoji ke yi kan yan ta’addan na haifar da ‘ya’ya masu idanu.

Zamfara – ‘Yan bindigan da ke aikata ta’asa a Zamfara a halin yanzu suna ta guduwa sakamakon matakan tsaro da gwamnati ta dauka da kuma aikin sojoji da ke gudana.

Don sanya su cikin damuwa, Gwamnatin Tarayya ta rufe hanyar sadarwar waya yayin da gwamnatin jahar ta rufe wasu kasuwannin da ke aiki a kowane mako.

Ko da yake an samu wasu koma-baya, da yawa sun ce aikin ya cimma nasara sosai.

Da yake tsokaci kan wannan, Gwamna Bello Matawalle ya ce yawan hare-haren da jami’an tsaro ke kaiwa ‘yan fashi ya sa sun sake neman sulhu da gwamnati.

Ya lura cewa wasu daga cikin ‘yan fashin suna tserewa daga Zamfara zuwa wasu jahohi sakamakon sabbin matakan tsaro da gwamnatin jahar ta bullo da su.

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa ta gano wasu sabbin wuraren da ‘yan bindigar ke yada zango tun lokacin da aka fara yi masu ruwan bama-bamai.

Daga cikin wuraren da suka tsere, a cewar majiyoyi akwai:

2. Lambar Tureta a Sokoto

3. Birnin-Gwari a Kaduna

Rekeb, wani sanannen ɗan fashi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust da komawar wasu daga cikin yan bindigar, amma ya yi alfahari da cewa shi da sauran manyan masu ta’addanci suna ci gaba da kasancewa a cikin “sanannen wurin da suke a Zamfara”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here