LABARI DA DUMI-DUMINSA: Ana Musayar Wuta Tsakanin Mayakan ISWAP da Sojoji a Borno

 

Kamar yadda labarai daga majiya mai karfi ta sanar, ana musayar wuta tsakanin ‘yan ISWAP da sojojin Najeriya.

Hakan na faruwa ne wurare biyu mabanbanta amma a lokaci daya a jihar Borno da ke arewa maso gabas – Majiyar ta sanar da jaridar HumAngle cewa lamarin na faru ne a yanzu da yammacin ranar Lahadi Mayakan ta’addanci na ISWAP, wadanda wani bangare ne na Boko Haram a halin yanzu suna musayar ruwan wuta tsakaninsu da dakarun sojin Najeriya.

Hakan yana faruwa ne a wurare biyu mabanbanta da ke Tungushe kusa da Monguno da kuma karamar hukumar Damboa. Kamar yadda majiya wacce ganau ce ba jiyau ba ta sanar da jaridar HumAngle, hakan yana faruwa ne a yammacin ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020. Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here