Wutar Kyandir Tayi Sanadiyyar Kona Gidaje 30 a Port Harcourt

 

Wutar kyandir tayi sanadiyyar asarar gidaje akalla 30 da sauran dukiyoyi masu kimar miliyoyi a wuraren Okwelle na Mile 2 a Port Harcourt.

An tattara bayanai akan yadda wata mata ta bar kyandir a kunne wanda yayi sanadiyyar kazamar gobarar wacce ta fara tun karfe 6:30am.

Matasan anguwar sun taru suna amfani da ruwa da omo don kokarin kashe wutar kafin motar kwana-kwana ta iso ta kashe wutar.

Rivers – Kyandir ya yi dalilin gobarar datayi sanadiyyar kone gidaje fiye da 30 da dukiyoyi masu kimar miliyoyi a wuraren Okwelle dake Mile 2 a Port Harcourt.

Kamar yadda The Nation ta wallafa, an tattara bayanai akan yadda wata mata ta bar kyandir a kunne wanda yayi sanadiyyar wata kazamar gobara wacce tun karfe 6:30 na safe take ci.

Yaya wannan kazamar gobara ta faru?

Mun tambayesu ba’asin wutar sai suka ce wata ce ta kunna kyandir tun karfe 6am wutar take ci sai da ko ina ya cinye. Shiyasa kaga duk an taru.

Ina nan da yarana muna kokarin ganin mun kashe wutar. Sannan mun ga ‘yan kwana-kwana shine muku turasu Okwelle don su kawo dauki. Yanzu haka suna kokarin kashe wutar.

Me ganau suka ce kan gobarar?

Wani mazaunin yankin, Christain Alali ya ce wutar ta kara ruruwa ne sanadiyyar irin kayan alatun da suke cikin gidajen, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa:

Kasan akwai katako da yawa a wurinnan. Kafin masu kashe wuta su iso gaba daya gine-ginen sun kurmushe.

Idan ba don masu gadin nan ba da matasa, da kafin masu kashe gobarar su iso komai ya gama lalacewa.

Wata mazauniya yankin ta bayyana yadda komai nata ya kone kuma ta roka gwamna Nyesom Wike ya tallafa musu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here