Yadda Zaka yi Rijistar JAMB a 2021
Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara sayar da fom ranar Asabar ɗin da ta gabata.
JAMB ta dakatar da fara yin rijistar ne tun baya saboda wasu matsaloli da ba’a yi tsammani ba a kan lambar zama ɗan ƙasa NIN.
Akwai sabbin dokoki da hukumar ta ɓullo da su a wannan shekarar wanda doƙe saika cika su kan ka yi rijista Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara yin rijistar jarabawar ta 2021 ranar Asabar.
Hukumar ta sanar da fara rijistar zana jarabawar neman gurbin shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) da kuma rijistar DE.
Hukuncin fara rijistar yazo ne awanni 48 bayan hukumar ta dakatar da shirin saboda wasu matsaloli data samu kan lambar zama ɗan ƙasa NIN. Amma a wani saƙo da mai magana da yawun JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar ya ce an warware matsalar saboda haka yanzun an fara rijistar.
Dalla-Dalla yadda zaka yi rejistar jarawar ta bana ba tare da matsala ba.
1. Ka tambatar da kana da Lambar waya da E-Mail
Read Also:
Yana da matuƙar muhummanci ya kasance kana da lambar waya, da kuma E-mail masu aiki ba tare da tangarɗa ba. Saboda kowanne ɗalibi na da buƙatar turawa da kuma amsar saƙo daga JAMB a ya yin gudaɓar da rijistar sa.
2. Lambar jikin ƙatin ɗan kasa wato NIN
JAMB ta maida amfani da NIN ya zama wajibi g duk mai son zana jarabawar a wannan shekarar. Sabida haka ya zama wajibi ka mallake ta kafin ka yi rijista.
3. Ka ziyarci shafin JAMB
Bayan ka tabbatar da ka mallaki email da NIN, saika ziyarci shafin JAMB, ka buɗe ma kanka kundin aje bayanai kafin kaje ka siya takardar rijista ɗin.
4. Ka duba cancantar ka na zana jarabawar bana a JAMB iBass
Bayan ka buɗe kundin aje bayananka a shafin JAMB, akwai buƙatar ka duba shafin don tabbatar da shin ka cancanci ka zana jarabawar ta bana, zaka iya duba wannan a ‘JAMB iBass’ dake shafin na JAMB.
5. Sai kuma ka sayi Lambar sirri wadda zata baka damar yin rijista.
Bayan ka tabbatar da ka cancanci ka zauna jarabawar ta wannan shekara, sai kuma kaje ka siya lambar sirri (JAMB E-PIN) waɓda zata baka damar yin rijista, zaka iya siyan E-PIN din a bankuna ko a wuraren da hukumar ta amince da su.
6. Cibiyar CBT
Bayan kammala dukkan haka, saika ziyarci ɗaya daga cikin wuraren zana jarabawa a na’ura mai ƙwawalwa (CBT Centre) waɗanda JAMB ɗin ta tantance kuma ta amince da su tare da dukkan bayanan ka da kuma PIN ɗin daka siya don yin rijista.