Yaduwar Cutar Korona Zata Karu a Watan Janairu – NCDC
NCDC, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa, ta ce ‘yan Nigeria sun yi uwar watsi da matakan dakile yaduwar annobar korona.
Shuagaban NCDC ya ce ‘yan Nigeria su shirya domin za’a fuskanci hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona daga satin nan.
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Nigeria (NCDC) ta yi gargadin cewa za’a sha wahala a cikin watan Janairu mai zuwa saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da za’a fuskanta.
NCDC ta ce za’a fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da kwayar cutar za ta harba saboda yadda jama’a suka yi burus da matakan kiyayewa yayin bukukuwan hutun da aka samu, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Read Also:
A cewar NCDC, makon da ya gabata ya kasance daga cikin mafi ban tsoro saboda tashin gwauron zabi da alkaluman mutanen da suka kamu da cutar ya yi.
A saboda haka, cibiyar ta gargadi ‘yan Nigeria tare da yi musu tunin cewa su shirya girbar abinda suka shuka tunda suka yi watsi da dukkan sharuda da matan kiyayewa yayin hutun bukukuwan kirsimeti da karshen shekara.
Darekta Janar na NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, shine ya fadi hakan a Abuja yayin taron kwamitin PTF akan korona na ranar Talata.
“Mun fuskanci sati mafi muni tun bayan barkewar annobar korona, amma sai gashi cikin makon da ya biyo bayansa, jama’a sun yi watsi da duk wasu matakan kiyayewa.
“Ga hotuna da bidiyon taron jama’a a wurin shagulgulan biki suna ta yawo a dandalin sada zumunta, abin haushi da tayar da hankali.
“Za’a ji jiki a watan Janairu, babu wani abin mamaki idan an fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da zasu kamu da kwayar cutar korona sakamakon cudanya da saba ka’idojin da gwamnati ta gindaya,” a cewarsa.